Friday, 16 June 2017

NA TSINCI NAIRA ₦500 KOZAN IYA AMFANI DA ITA BATARE DA CIGIYA BA ???

Tags

NA TSINCI NAIRA ₦500  KOZAN IYA AMFANI DA ITA BATARE DA CIGIYA BA ???

Tambaya ?
Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya tsinci Naira 500, kuma baiga wadanda zai yiwa cikiya ba...

Yaya kamata yayi da wannan kudin tsintuwar ?

Suna ajiye yanzu haka kusan wata daya kenan.

(Daga Ibraheem Ishaq Rano).

AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

To dan uwa idan mutum yayi tsintuwa ya wajaba a gareshi yayi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma idan mai ita yazo daga baya zai biya shi.

Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisinsa mai lamba ta: 5761.

Amma idan abin daya tsinta dan kadan ne bashida yawa, to ya halatta yayi amfani dashi koda baiyi cigiya ba.

Saboda abin da aka rawaito cewa:

Annabi (s.a.w) yaga wani dabino akan hanya, sai yace:

In banda ına tsoron kona sadaka ne da naci.

Muslim ya rawaito a hadith mai lamba ta:2527.

Sai hadişin ya nuna dan karamin abu baya bukatar cigiya.

Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da bata bukatar cigiya.

Wasu sun ce za'a koma al'adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to idan an tsince shi baya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa:

Bai wajaba mutum yayi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shiba, wato daya bisa hudun dinare.

Haka nan sayyadina Aliyu (R.A) ya tsinci dinare daya yayi amfani da ita batare da yayi cigiya ba.

Abin daya gabata yana nuna cewa:

mutukar baka sami mai Naira (500) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta kayi amfani da ita batare da cigiya ba, tunda ba kudine mai yawa ba, kuma mai ita bazai kwallafa rai Akantaba.

Domin neman karin bayani aduba: Al-mugni 6/351.

Allah shine mafi Sani.