Friday, 16 June 2017

Hukuncin wanda ya kwanta barci yayi mafarki kuma ga ranar anayin sanyi

Tags

☀TAMBAYOYIN TAFARKIN TSIRA☀

««fatawa ta 81»»

Assalamu Alaikum

Malam menene hukuncin wanda ya kwanta barci yayi mafarki kuma ga ranar anayin sanyi bayadda zai yadafa ruwa ga asuba tayi shin zai hakura da sallar asuba ne ko kuwa ?

(Daga Nafi'u Abdullahi Masaya).

AMSA
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.

GASKIYA wannan tambayar kamar akwai son rai aciki.

Ya kamata matasanmu su fahimci cewar SALLAH FA ITACE MAFI GIRMAN IBADAH.

Duk wanda yakula da ita, to hakika ya kula da addininsa.

Wanda ya rusheta ta hanyar son rai ko kasala, ko jahilci, to hakika YARUSHE ADDININSA.

Wanda ya tsinci kansa acikin yanayi na mafarki, irin wannan taimama zaiyi, tunda zuwar masa yayi bagatatan batare daya shirya ba.

Saidai kuma ita taymama ba'a yinta saida Karkarfan dalili.

Kamar idan ya zamto babu ruwa, ko kuma idan ya zamto akwai ruwan amma ba za'a iya amfani dashi ba saboda tsoron mutuwa ko kuma motsawar wata jinya. Da sauransu.

Amma don kawai kanajin sanyin hunturu, wannan bai isa hujjar da zaisa kayi taymama ba.

Domin kuwa da ache wani uzurinka na duniya zai bujuro, to hakika dazaka fita kayi wanka domin tafiya wancan Uzurin.

Sannan awannan zamanin namu muna da bambanci da zamanunnukan da suka wuce:

muna da ashana.

Muna da Risho.

Muna da Laiyta.

Muna da heater.

Kaga kenan idan ma kana tsoron sanyin ne, to ai agidanku ko acikin dakinka ma ba za'a rasa abin dafa ruwa ba.

Don haka ya kamata muyi kokari mu kula da Tsarki da Sallah.

Domin kuwa ita ce farkon abinda za'a yi Mana Hisabi akai.

WALLAHU A'ALAM