WANENE SA'AD BN ABI WAQQAS ???
=====================
Sa'ad Bn Abi Waqqas (R.A) Yana 1 daga cikin wadanda suka fara karbar musulunci.
kuma yana daya daga cikin mutane 10 da aka yiwa bushara da Aljannah tun suna raye a duniya.
Kuma yana 1 daga cikin mutane shida masu zaben khalifa.
Dayane daga cikin yardaddu a wajen Annabi [SAW].
Ya halarci yakin Badar da dukkan yakoki tareda
Annabi [SAW].
Yana cikin jarumai maharba na Annabi [SAW].
Shine wanda yafara harba kibiyar sa saboda Allah.
Annabi [SAW] yayi masa addu'a cewa:
A duk lokacin da yayi harbi yana mai cewa:
"Ya Ubangiji kadatar da harbin sa, kuma ka amsa addu'ar sa".
Sa'ad (R.A) shine ya jagoranci musulmai a zamanin khalifancin Sayyaduna Umar (R.A) wajen rusa Daular Farisa.
Shine yabude babban birnin Farisa "Mada'in" yakuma kafa garin Kufa.
Sa'ad yayi rayuwa mai tsawo cikin tsananin biyayya ga Allah da gudun duniya.
Ance shi mutum ne mai tsananin tsoron Allah da yawan kuka musamman ma idan Annabi [SAW] yana yimusu huduba da wa'azi.
Ya Allah ka kara masa yarda da aminci bisaga aikin da yayiwa Addinin Musulunci.