Tuesday, 19 December 2017

WANENE "ABDULRAHMAN BN AUF" ???

Tags

WANENE "ABDULRAHMAN BN AUF" ???

NASABARSA:
Sunansa Abdurrahman bn Auf bn Harith bn Zuhurata.....

MUSULUNTARSA:
Ya musulunta da wuri tun kafin Manzon Allah (saw) ya shiga gidan Arqam.

Abdurrahman yayi hijra sau biyu zuwa Habasha, kuma yayi hijira zuwa Madina.

Bayan anyi hijira daga Makkah zuwa madina.

Abdurrahman ya halarci duk wata marhala tare da Manzon Allah (S.A.W).

A ranar yakin Badar shine yakashe Qaton kafirinnan mai suna:

"Umair bn Usman Attamimiy"

A ranar yakin Uhudu Abdurrahman yabawa Manzon Allah (saw) kariya, har saida akayi masa rauni guda ashirin da tara (29) daga saran takobi da sukar mashi.

Manzon Allah (saw) yahada 'yan uwantaka tsakanin Abdurrahman bn Auf da Sa'ad bn Rabi'a Al-ansariy.

Sai Abdurrahman yazama babban dan kasuwa, kuma mafi arzikin cikin sahabbai.

Yayin da Manzon Allah (saw) yayi niyar fita yakin tabuka, sai yayi kira ga muminai domin kowa yakawo gudun mawarsa.

Sai Abdurrahman yakawo dinare duba arba'in (kimanin naira milyan dubu da milyan dari hudu a yanzu).

Sannan yabada dokuna dari biyar taka haye da rakumi dari biyar taka haye (kimanin nera milyan dari biyu a yanzu).

Dukkansu domin neman yardar Allah.

Saboda irin wannan taimako da Abdurrahman yabawa addinin musulunci, sai Manzon Allah (saw) yace:

"Ya Allah ka shayar da Abdurraman ruwan salsabil na Aljannah".

Kasancewar Abdurraman yafi kowa arziki cikin sahabbai, kuma yafi kowa yawan kadara, wata rana yayi sadaka da dinare dubu, sannan yayi sadaka da azurfa dubu biyar, ya 'yanta bayi ashirin da biyar duk a rana daya.

Wannan sahabi mai daraja yanada falala mai tarin yawa, yana daya daga cikin sahabbai goma wadanda aka yiwa bushara da Aljanna tun suna suna raye.

Hakika wannan sahabi mai daraja yabada misali mai fadi yalwatacce wajan koyi.

Bayan gwagwarmaya da dukiyarsa da takobinsa, sai numfashinsa mai tsarki yafita zuwa ga Allah Ubangijin bayi.

Ma'abocin haske guda biyu wato khalifa Usman shine yayi masa salla.

Aliyu bn Abu-Dalib (ra) da Sa'ad bn Abi-Waqqas (ra) sune suka kwantar dashi cikin qabarinsa (RA).

Allah kaqara tsira garesu kabamu ikon yin koyi dasu.