NA AURI AMARE BIYU A RANA DAYA, YAYA YA KAMATA NAYI WAJEN TAREWA ???
Tambaya : Assalamu alaikum.
Malam mutum ne ya auri mata biyu (sangaya) rana guda, to dakin wacce zai fara shiga ???
Nagode Allah ya karawa malam imani.
(Daga Isma'il Mukhtar).
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa wasu daga cikin malamai sun karhanta auren mata biyu a yini daya, saboda hakan zai kawo matsala wajan bawa matan hakkinsu na kwana, saboda duk wacce aka fara da ita, to dayar zata cutu, saidai idan hakan tafaru, to zai fara ne da wacce ta fara shigowa gidan, idan kuma sun shigo tare ne sai yayi musu kuria.
Domin neman Karin bayani sai aduba: Al-kafy Na Ibnu Khudaamah shafi na : 981.
Allah shine mafi sani.
Tuesday, 19 December 2017
NA AURI AMARE BIYU A RANA DAYA, YAYA YA KAMATA NAYI WAJEN TAREWA ???
Tags
Artikel Terkait
Post a Comment
Subscribe to:
Post Comments (Atom)