Menene hukuncin wanda akayi masa sallama amma yaqi amsawa, kodai saboda girman kai ko kuma saboda wani dalili ???
(Daga Hafiz Ibrahim).
AMSA:
=====
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
kada kadamu kaida kayi masa sallamar bakayi asara ba.
Aduk lokacin da kayiwa mutum sallama, idan ya amsa kana da lada yana da lada, idan kuwa yaqi amsawa wadanda suka fishi daraja da mutunci (mala'ikun rahama) sun amsa maka.
Akwai wanda za'a yiwa gaisuwa 'Assalamu Alaikum'.
Yaqi amsawa, saboda shi (yana ganin) ba dama ne, yana jijji da kansa, ko kuma wanda za'a gaishe shi saboda wani banbanci na aqida, shi bai yarda da imanin kaba.
Don haka sai yaqi amsawa.
Kaga wannan kuwa jahilci ne yake kawo haka.
Wannan ba dabi'a bace ta "Ahlus Sunnah".
Don haka idan kayi masa sallama ya amsa kai dashi kunyi tarayya cikin lada, in yaqi amsawa kuwa to, wannan shine yayi asara, kai kam bakayi asara ba.
Sannan mala'ikun rahma sun amsa maka, Kamar yadda hadisai da sunnah suka koyar.
WALLAHU A'ALAM.
Allah yabamu ikon gyarawa.