MANZON ALLAH (S.A.W) YACE:
Lallai acikin aljannah akwai wata kasuwa da ake zuwanta a ranar juma'a Idan mutane sukaje wannan kasuwa sai wata iska tazo musu ta arewa saita shafi fuskokinsu da rigunansu, Sai suqara yin kyau
Sai sukoma wajen iyalansu.
A lokacin suma sun qarayin kyau
sai iyalansu suce musu wallahi anqara muku kyau.
Sai suma sukalli iyalansu suga sunqara kyau.
Sai suma suce musu lallai kuma anqara muku kyau bayan fitarmu.
Sahih Muslim:2833
Ya Allah kasa muna cikin wadannan salihan bayi.