Thursday, 14 December 2017

*HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE LAFIYA*

Tags

*HANYOYI 26 DOMIN ZAMA DA IYAYE LAFIYA*
-----------------------------------------------

1. Ka ajiye wayarka yayin da iyayenka sukeyi maka magana.

Kar ya zamanto suna yi maka
magana, kai kuma kana danne-danne awayarka.

(Browsing ko Chatting).

Wannan Rainin wayo kenan.

2. Ka rika neman shawara a wajensu.

Kuma idan sun baka shawara karika dauka kana amfani da
ita.

Koda akan neman aurenka ne, girmamawar kenan.

3. Karka rika tsoma baki acikin maganarsu, harsai idan sunyi maka izini.

Kuma duk zancen da zakayi dasu, wajibi ne kayi amfani da zababbun kalmomi na musamman.

4. Koda an samu rashin fahimtar Juna a tsakaninka dasu, karka yarda su fahimci ranka yabaci, ballantana harka furta musuvwata mummunar kalma wacce zata Sosa musu rai.

5. Ka rika yaba musu a bisa dukkan abinda sukayi maka komai kankantarsa.

Koda addu’a sukayi maka, to lallai ka tsaya kayi musu godiya
a bisa wannan domin wadansu tsine musu akeyi.

6. Karika girmama ‘Yan uwansu da abokansu.

Karika ziyartarsu kana Kyautata alakarka dasu.

Domin girmamasu kamar girmama mahaifan nakane.

7. Duk lokacin da wani abin farin ciki ya sameka, to kafara gayawa mahaifanka kafin ka gayawa
kowa.

Amma idan abin bakin ciki ne, kar kayarda suji abinda hankalinsu zai tashi.

8. Kar kamanta da muhimman gudunmuwar da Iyayenka suka bawa rayuwarka.

Ka rika ji a cikin ranka cewar babu abinda zakayi ka iya biyansu.

9. Wani lokacin zasu gaya maka labari kuma washegari su sake maimaita maka, sun manta cewa sun riga sun gaya maka.

To amma duk da haka karka nuna musu kosawarka wajen
sauraronsu.

10. Abinda yawuce ya riga yawuce.

Karka rika zargin iyayenka ko tuhumarsu da wani laifi.

Kuma kar ka rika tuno musu wani mummunan labari.

11. Kar karika shiga gaban mahaifinka idan zakuyi tafiya.

Kuma duk lokacin da kake zaune tare dashi a gida ko a Mota, Kazauna cikin ladabi.

Ka tashi tare da ladabi.

12. Kaguji zagi ko bugun kannenka Ko jikokin gidanku akan kananan abubuwa.

Watakil yin hakan zai sosa zuciyar Mahaifanka.

13. Ka rika amfani da Murya mai taushi, lafazi mai taushi, Kallo mai taushi a duk lokacin da kake tare da Mahaifanka.

Kuma kar ka daga muryarka sama da tasu.

14. Ka kiyaye Sirrin mahaifanka.

Karka rika daukar labarin da zai janyo zubewar Mutuncinsu kana fadawa wa mutane.

15. Mahaifanka sune abu mafi daraja, mafi tsada wanda ka mallaka.

Don haka ka lailayesu, ka kula
dasu fiyeda yadda kake kulawa da kanka.

16. Indai kana da hali, karka yarda kaci wani abu mai dadi ba tare da ka saya musu irinsa ko
fiye dashi ba.

Karka yarda kasha wani abu mai sanyi mai dadi wanda su basu sha irinsa ba.

17. Ka kyautata musu suturar da suke sanyawa.

Da kuma wajen kwanansu da abincinsu.

Ka tabbatar ka ingantashi fiye da naka na kanka.

18. Duk lokacin da basu da lafiya, Karka wakilta wani ya kula dasu.

A’a kaine zaka kula dasu.

Ka kyale duk harkokinka katafi yazuwa garesu.

Kar kamanta lokacin da kayi zazzabi sanda kana yaro, ai ba su wakilta maka kowa ba, su suka kula dakai.

19. Karka rika jiran wai sai sun rokeka abu sannan kayi musu, a’a ka tabbatar kanayi musu tun kafin su nema.

20. Idan kana zaune gida guda ko gari guda tare dasu, Karka yarda Safiya ta wuce baka je kagaida su ba.

Idan kuma kana aiki a wani garinne, to koda duk Karshen mako ne, Sai kaje ka duba su kuma ka nemi afuwarsu bisa rashin ganinka da ba su yi ba.

21. Ka kasance ko yaushe cikin yin addu’a agaresu, ba wai sai a gurbin Sallah ba.

Kuma ka rika neman afuwarsu da zarar ka fahimci wani
abu ya sosa musu rai.

Koda ba kaine ka aikata ba.

22. Idan kuma sun rasu, to kar kadena addu’a a garesu har karshen rayuwarka.

Kuma ka rungumi zumuncinsu ya zama naka.

23. Ka rika shiga sha’anin kannenka da yayyenka
gwargwadon yadda zaka kyautata alakarka da su.

Kar karika nuna ‘Yan Ubanci ga wasu daga cikin kannenka.

Yin hakan zai sosa zuciyar mahaifinka.

24. Ka rika kiran mahaifanka da sunaye na girmamawa, kar ka rika kiransu da sunayensu.

Watakil yin hakan zai zubar da mutuncinsu a gaban mutane.

25. Idan sun samu rashin fahimtar Juna a tsakanin junansu, Kayi kokari ka daidaitasu batare da kagoyi bayan kowanne daga cikinsu ba.

26. Ka kiyaye kar ka yarda ka fifita matarka akan iyayenka duk irin son da takema.

Ana chanjin Mace, amma ba’a chanza iyaye.

Ya Allah ka jikan Iyayenmu ka gafarta musu.

Ka kyautata makwancinsu ka haskaka Kaburburansu.

Kayi musu rahama kamar yadda suka ji kanmu tun muna kanana.

Allah kabamu ikon biyayya a garesu