DOMIN KE DA MIJINKI.
««fitowa ta 9»»
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Allah sarki, yau dinnan muke tsallake darasin mace tagari zuwa miji na qwarai.
Kwance tashi ba wahala, saidai shawarata dake itace:
Kisani bazai ta6a yiwuwa kiyi addini da jahilci ba.
Mace mai addini tana tareda iliminta ba jahila bace, duk yadda mijinki yakai da ilimi bazaisa kishiga aljanna ba sai in kinyi aikin dazai kaiki aljannar، kamar yadda shima yakeyi, kowa ta kansa yakeyi a lahira.
Wannan nema yasa matar Annabi Ludht (A.S) tashiga wuta، matar Fir'auna (L.A) tashiga aljanna.
Kunga kenan duk ilimin mijinki nasane kema kinemi naki, idan Allah ya qaddara rasuwarsa kinada saninki, haka duk ibadarsa tasace kema kiyi taki.
Tabbas Annabi (S.A.W) ya warewa mata rana guda daya ariqa koyar dasu.
Kuma Allah (S.W.T) da KanSa yace:
واذكرن ما يتلى في بيوتكن من آيات الله والحكمة
Ku (mata) kuyi darasin abin da ake karantawa a dakunanku na ayoyin Allah da hikima wato (hadisi).
Ahzab 34.
Wajibin mace ne tanemi ilimin dazai kaita aljanna.
Namiji bai da hujjar dazai ajiye ta cikin jahilci, ko dai ya koyar da ita, koya kawo wanda zai koya mata koya barta tatafi inda zata koya, idan Allah yaso bawansa namiji ko mace yakan sanar dashi addininsa ne.
Don haka Allah (S.W.T) yayi tambaya:
قل هل يستوي الذين يعلمون والذين لا يعلمون
Kace shin wadanda suke da ilimi zasuyi daidai da marasa ilimi ?
Sura Zumr 9.
Don buga misali Annabi ya barmu damu kar6i rabin addininmu a wajen iyalinsa, da ace bata dashi da hakan bai faru ba. Subhanallah!
A yau matan malamai sunfi kowa jahilci saidai Allah ya gyara, ance:
"Kai baka koyar da ita ba, baka kawo mata mai koyar da ita ba,
Kuma a haka kakeson biyayya irin ta addini, da ibada irin ta masana, tana da hakki akanka yalla6ai kaji tsoron Allah ka sanar da ita addininta.
Ke kuma kiriqi 'ya'yanki, ki koya musu fadin gaskiya da ikhlasi a cikin ayyukansu, kar kiyi sakaci in kikaga danki yafara cin abinci bai ce bismillahi ba, ko shiga daki ba sallama, ko daukan abin da ba ai masa izini ba koda kuwa 'yan uwansa sun gaya masa cewa nasane, ki koya musu tsafta, 'yarki ta koyi ayyukan gida tun tana qarama har girmanta, karki yardar mata da barcin rana bayan akwai aiki a gida.
Banda zagi a gaban yaranki, ko mummunar magana, in kikaji a bakin wani cikinsu koda sau Daya ne ki dauki mataki.
Ki koya musu yiwa iyayensu addu'a kowane lokaci.
Ki nuna musu darajar babansu da matsayinsa.
Ki koyawa 'yarki mace tun tana qarama son aikin gida, ki sabar mata da kwalliya, ki ladabtar da ita bisa tafarki, ki koya mata rufe kwalliya a waje da dadin magana.
Kiriqa nuna mata yadda kike yiwa mai gidanki don yazama mata darasi.
Kiriqa gayawa danki kyawawan halayen mahaifinsa tareda fatan cewa zai fishi a nan gaba.
Duk wanda yayi abin qwarai ki yaba masa, wanda yayi kuskure ki ladabtar dashi.
Ki koya musu son addini da kamewa, da wadatar zuci, ki nunawa 'ya'yanki son addini.
Anaso mace ta tsaya a matsayinta namiji shima haka, ki koyar dasu son karatun addini da riqo dashi, da matsayin imani da Ikhlasi.
INA TAYAKI MURNAR ZAMA MACE TA GARI.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.