ALLAH YAYI TANADI NA MUSAMMAN DOMIN MASU ZUWA SALLAH AKAN LOKACINTA.
ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﻋَﻦْ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲِّ
ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ ﻣَﻦْﻏَﺪَﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﻤَﺴْﺠِﺪِ ﻭَﺭَﺍﺡَ
ﺃَﻋَﺪَّ ﺍﻟﻠَّﻪُﻟَﻪُ ﻧُﺰُﻟَﻪُ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﻛُﻠَّﻤَﺎ ﻏَﺪَﺍ ﺃَﻭْﺭَﺍﺡ
««fassara»»
An kar6o daga Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa:
Manzon Allah (s.a.w) yace:
“Duk mutumin da yake zuwa Masallaci da safe da yamma a koda yaushe, to hakika Allah zaiyi masa tanadin wani waje na musamman acikin Aljannah da safe da yamma a koda yaushe.”
Hadisin yana cikin: Sahih Bukhari hadith mai lamba 631, ko kuma Hadisin Sahih Muslim na 669.
Ya ALLAH ka sanya mu, acikin irin wadannan mutanen daka yiwa wannan tanadin a ranar gobe Al-kiyama.
Ya ALLAH ka gafarta mana, ka gafartawa
iyayen mu da suka rigamu gidan gaskiya.
Ya ALLAH ka karbi tubanmu a koda yaushe.