Wednesday, 20 December 2017

ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21.

Tags

ALAMOMIN CIKAWA DA IMANI GUDA 21.

Wannan duniyar cike take da rikici, da musifu, da bala'o'i, da tashin hankali da jarrabawa, da matsaloli, babbar nasara shine, cikawa da imani.

Malamai sunyi bayanai game da wasu alamomi, idan mutum yacika dasu, anayi masa fata nagari.

Sune:

1- cikawa da kalmar shahada.

2- mutuwa da gumin goshi.

3- mutuwa a daren Juma'a ko ranar Juma'a.

4- Shahada a filin yakin daukaka Addinin Allah.

5- Mutuwa a tafarkin Allah.

6- mutuwa da Annoba.

7- mutuwa da sababin ciwon ciki.

8- mutuwa ta dalilin nutsewa a ruwa.

9- mutuwa karkashin gini.

10- mutuwa da kunar wuta.

11- mutuwa da ciwon kaluluwa.

12- mace ta mutu a wajen haihuwa.

13- wanda aka kasheshi wajen tsare dukiyar sa,

14- wanda aka kashe shi wajen tsare iyalansa.

15-wanda aka kashe shi, saboda addinin sa.

16- wanda aka kasheshi wajen kare kansa.

17- wanda ya mutu da ciwon tarin fuka.

18- wanda aka kashe shi, akan hakkinsa.

19- wanda ya mutu wajen gadin addini da dukkiyar
Al'umma.

20- wanda ya mutu yana cikin aikin alkhairi, kamar sallah dawafi, azumi sujjada, da makamantansu.

21- wanda yamutu
mutane suna tayi masa sheda tagari.

Dalilan wadannan bayanai daga littafin Allah da
sunnar Annabi (s.a.w) suna cikin littafin.
''Ahkamul Janaiz'' na ''Shaik Albaniy'' da ''Salatul Mumina'' na Dr Saeed alqahdaniy.

Allah ya Tabatar damu akan addinin MUSULUNCI Har karshen rayuwar mu.

Allah kasa mucika da imani.